A yayin wata ganawa da manema labarai a Abuja Komrade Imrana wada Nas dake zama Shugaban hadaddiyar kungiyar matasan arewacin Najeriya kuma shugaban rundunar talakawan kasar ya bayyana cewa, bisa hasashen da suka yi da duba cikin yanayin da jam’iyyar APC ke ciki da wuya jamiyyar ta iya gudanar da babban taronta dake tafe a watan Febrairu mai zuwa bisa la’akari da rarrabuwan kawuna da rikici da ya mamaye ‘yayan jam’iyyar
A cewarsa, “jam’iyyar APC tana cikin tsaka mai wuya, kuma in ba taimakon Allah jam’iyyar ta samu ba, ba za ta iya kai labari ba duk da ta fitar da ranar gudanar da babban taronta na kasa a cikin watan Fabrairu
A ranar 19 ga watan Janerun da muke ciki ne dai kwamitin riko na Jam’iyyar APC ta fitar da sanarwar cewa, zata gudanar da babban taronta a ranar 26 ga watan gobe na Febrairu, kazalika ta bayyana tsare tsaren da zata bi wajen kai ga gudanar da taron
A baya dai an yi ta kai ruwa rana sakamokon rikice-rikice da rarrabuwar kawuna ya dabaibaye jam’iyyar inda har wasu ’yan jam’iyyar suka gurfanar da kwamitin rikon kwarya na shugabancin Jam’iyyar ta kasa a gaban babbar kotun Abuja domin ta hana a gudanar da babban taron jam’iyyar, bisa kalubalantar sahihanci da kuma cancantar kwamitin riko na Jam’iyyar na kasa da ke karkashin jagorancin gwamna mai Mala Bunin na Jihar Yobe.
Saurari karin bayani cikin wannan sauti.