Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Legas Ta Ayyana Kawo Karshen Zango Na 4 Na Cutar COVID-19


Allurar rigakafin Covid 19
Allurar rigakafin Covid 19

A dai jihar ta Legas aka fara samun bullar cutar ta COVID-19 bayan da aka samu wani dan Italiya da ita.

Gwamnatin jihar Legas ta bayyana kawo karshen zango na 4 na illar cutar coronavirus da ta fara aikin magance cutar a ranar 7 ga Disambar bara.

Kwamishinan lafiya na jihar Akin Abayomi ya bayyana haka da nuna an samu raguwar masu kamuwa da cutar.

Abayomi ya ce an samu raguwar kamuwa daga zangon na hudu daga kashi 29.3% a watan Disambar bara zuwa kashi 1.9% a wannan wata na Janairun bana.

A cewarsa, masu kwanciya a asibiti yanzu da kashi 2 cikin dari sannan kuma an samu raguwa sosai na masu mutuwa daga cutar da kashi 0.71

Kwamishinan ya bukaci jama’a su yi kokarin yin rigakafin cutar ta annoba da kuma daukar sauran matakan kare kai.

In za a tuna an fara samun cutar ta farko ta korona a Najeriya daga jihar ta Legas ne.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG