Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hedkwatar Tsaron Najeriya Ta Tabbatar Da Mika Wuyan Sama Da Yan’ta’adda 863


Zaman Majalisar dattijai na tantance hafsoshin sojin Najeriya.
Zaman Majalisar dattijai na tantance hafsoshin sojin Najeriya.

Hedkwatar tsaron Najeriya DHQ ta ce ta halaka 'yan ta'adda 49 a karkashin ayyukan sojinta yayin da wasu 'yan ta'adda 863 da iyalansu sun mika makaman su a makonni biyu da suka gabata.

Daraktan yada labarai, Bernard Onyeuk ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai kan ayyukan sojin kasar a Abuja.

Onyeuko ya ce sojin rundunar Operation Hadin Kai sun halaka 'yan ta'adda 37, sun cafke 17 tare da samo miyagun makamai 117

Ya kara da cewa, sun kama motocin yaki hudu na 'yan ta'addan yayin da suka ceto mutum 16 da aka yi garkuwa da su duk a cikin makonni biyu.

Onyeuku ya ce 'yan ta'addan 863 tare da iyalan su da suka kunshi maza manya 136, mata manya 251 da kananan yara 486 sun mika wuya ga dakarun sojin. Ya ce sun mika kansu a wurare daban-daban da suka hada da Banki, Bama, Dikwa, Gwoza da Gamboru duk a jihar Borno.

Daraktan yada labaran ya kuma bayyana cewa, "Wannan ya yi sanadin halaka wasu daga cikin 'yan ta'addan yayin da wasu suka tsere da miyagun raunika. An samu wannan nasarar ne a ranar 14 ga watan Janairu yayin da aka samu bayanan sirri kuma aka aike sojin sama yankin da 'yan ta'addan ke taron su. Sojin saman sun yi wa 'yan ta'addan ruwan wuta ta sama,"

A wani aiki na sojojin, Onyeuko ya ce dakarun sun halaka 'yan ta'adda 12 tare da cafke masu basu bayanai 15. Ya kara da cewa an kwace makamai masu hadari tare da shanun sata 114, kazalika dakarun sun kwato miyagun bindigogi da kuma babura hudu sai suka ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su.

Onyeuku Ya bayyana cewa sojojin sun sami nasar sosai a wurere daban-daban a jihohin Adamawa da Yobe, kusa da tsaunin Mandara da kuma kan hanyar Damaturu zuwa Potuskum.

XS
SM
MD
LG