Majalisar dokokin Najeriya ta sake tura dokar zabe da ta yi wa gyaran fuska ga shugaba Buhari don amincewa da sanya mata hannu zuwa doka.
In za'a iya tunawa, shugaba Buhari ya ki sanya hannu kan dokar tun da farko, don ta kunshi yin zaben ‘yar tinke na fidda ‘yan takara daga jam’iyyu, lamarin da shugaban ya ce sha'anin tsaro da kashe kudi ne suka sa hakan bashi da alfanu.
Kazalika shugaban ya ce in an bar dokar yanda ta ke za'a takaita damar jam’iyyu na fidda ‘yan takara ta zabi daban-daban irin na tsarin dimokaradiyya.
Majalisar dokokin dai ta bi bukatun shugaban sau da kafa kan cire sashen da shugaban ke ganin ba shi da fa’ida, inda a yanzu ta bude damar jam’iyyu kan iya amfani da zabi daban-daban, da suka hada da ta hanyar wakilai, ‘yar tinke ko ma daidaitawa wajen fidda dan takara.
Shugaban ya na da wata daya daga yanzu don sanya hannu kan kudurin zuwa doka.