Kungiyoyin addinin Islama a Jamhuriyar Nijar sun yi kira ga bangarorin da ke ja in ja kan sabuwar dokar harajin kasar su zauna kan teburin sulhu don samar da zaman lafiya a kasar.
Hukumomi a jihar Zamfara sun tabbatar da mutuwar shugaban Fulani ‘yan bindiga da aka fi sani da Buharin Daji, wanda ke zama jigon rashin zaman lafiya ta hanyar kai hare-hare da satar shanu da kuma garkuwa da mutane a yankin.
Jami’an tsaro a jamhuriyar Nijar sun kama wasu mutane uku ‘yan asalin kasar Ghana, ‘dauke da makamai iri daban-daban.
Rundunar sojin saman Najeriya ta shirya taron bita na musamman ga ‘yan jaridar dake bada rahotannin tsaro a kasar, kan yadda zasu hada rahotannin tsaro tare da kaucewa haddasa fitina.
Shugabannin tsaron Najeriya zasu bayyana gaban Majalisar Dattawa domin yin bayani kan yadda aka sace 'yan matan Dapchi da kuma kokarin da suke na ganin an nemo 'yan matan.
Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar bada agaji ta Red Cross sunce ba za a samu damar shigar da kayan agaji zuwa gabashin yankin Ghouta na Syria kamar yadda aka shirya yau Alhamis ba, saboda matsalar tsaro.
Jami'an gwamnatin Koriya ta Kudu na kan hanyarsu ta zuwa Amurka domin yi wa gwamnatin Trump bayani kan ganawarsu da shugaban Koriya ta Arewa.
Sa’oi kadan bayan da kotun tarayya ta ba da belin Maryam Sanda, matar da ake tuhuma da kashe mijinta, Bilyaminu Bello a Abuja, babban Birnin Najeriya, masana shari’a sun fara fashin baki kan wannan hukunci.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta umarci kwamishinonin ‘yan sandan jihohin kasar da su fara kwace rukunin makamai masu hadari ga jama’a, wadanda kuma jama’a ke mallakarsu ba bisa ka’idar ba.
An ba da belin Maryam Sanda, matar da ake zargi da kashe mijinta a watan Nuwambar bara, bayan da suka samu sabani a gidansu da ke Abuja, babban birnin Najeriya.
Gwamnatin jihar Filato ta ce zata bunkasa harkar noma don samarwa da al’ummar Najeriya abinci, a cewar gwamnan jihar Simon Lalong, yayin da yake ganawa da manema labarai da nuna musu taraktoci 400 da gwamnatinsa ta sayo don rarrabawa manoman jihar.
Noma Tushen Arziki
Wasu mazauna tsaunin Mambila a jihar Taraba, sun bayyana halin da suke ciki a yanzu, bayan wani sabon harin da aka sake kai musu a daren jiya Asabar lamarin da ya yi sanadiyar asarar rayuka ciki har da ta dabbobi.
Jami’ar Sule Lamido da ke garin Kafin Hausa a jihar Jigawa za ta samar da gurabe ga dalibai daga kasar Gambia, domin yin karatu a wasu darrusa.
Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya kare matsayin da gwamnonin APC suka dauka na nuna bukatar ganin shugaba Muhammadu Buhari ya sake tsaya wa takara a zaben 2019.
Babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya da ke Najeriya, Mr. Edward Kallon, ya tabbatar da cewa an hallaka ma'aikatan agaji uku a kauyen Rann da ke karamar hukumar Kala- Balge da ke jihar Borno, a daren jiya Alhamis sanadiyar wani harin da wasu suka kai a sansanin sojoji da ke yankin.
Wasu mahara da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun kai wa kauyen Milbu da Kaya hari, inda suka yi garkuwa da wasu mutane uku tare da sace mota guda.
Mutane sama da 10 aka kashe a wani tashin hankali da ya faru tsakanin makiyaya da al’ummar Bachama da suka kasance manoma, a yankin Gwamma na karamar hukumar Demsa a jihar Adamawa.
Masana a Najeriya, na ci gaba da tsokaci, kan cece-ku-cen da ke faruwa tsakanin jami’an tsaro game da yadda aka sace ‘yan matan Dapchi a jihar Yobe.
Sarki Salman na Saudiyya ya yiwa wasu manyan sojojin kasar da ministoci garambawul, a wani gagarumin sauyi da ya aiwatar a fannin tsaron kasar.
Domin Kari