Bisa ga dukkan alamu wannan yunkuri na rundunar ‘yan sandan kasar zai fuskanci babban kalubale, ganin yadda shirin ke shan suka daga al’umma da ma kungiyoyin.
Rundunar ‘yan sandan ta fitar da samfurin makaman da za a fara karbewa daga hannun mutane, inda kuma ta nemi goyon baya da hadin kai, sai dai kuma ‘yan yankin Niger-Delta sun fara bayyana ra’yoyinsu kan batun.
A cewar Agustun Silvanun, wannan maganar banza ce domin ko yayi rijistar makami ko baiyi ba wannan hanya ce da zai ci gaba da kare kansa da iyalansa, duba da irin halin da ake ciki a yankin da suke ciki, domin yan sanda ba komai zasu iya yi wajen ganin sun kare al’umma ba.
Muryar Amurka ta tuntubi rundunar ‘yan sandan jihar Rivers domin jin karin bayani kan wannan batu, inda rundunar ta tabbatar da samun wannan umarni sai dai kuma taki yin karin bayani kan yadda zata aiwatar da wannan aiki ba.
Rukunonin makaman da za a kwace daga hannun jama’a sun hada da bindigogi masu aman wuta da bama bamai da dai sauran makamai masu hatsari. Wani babban batu shine rukumonin da za a kwacewa wannan makamai sun hada da kungiyoyi irin na ‘yan bindigar Niger-Delta da kungiyoyin asiri da kungiyar Biafra da kungiyar ‘yan bangar siyasa da kuma rundunonin kato da gora da dai sauransu.
Domin karin bayani saurari rahotan Lamido Abubakar.
Facebook Forum