A cewar wata jami’a mai magana da yawun ofishin bada agaji na Majalisar Dinkin Duniya, Linda Tom, "MDD na ci gaba da samun rahotannin ci gaba da ake da fada a gabashin Ghouta, da kuma ruwan bama-baman da ake a Damascus, wanda ke zama hatsari ga fararen hula yana kuma hana isar da kayan agaji ga daruruwan mutanen dake cikin bukata."
Manyan motoci 46 sunyi nasarar kai kayan agaji bangaren Duma na gabashin Ghouta ranar Litinin, amma MDD da kungiyar Red Cross sun kasa ci gaba da shirinsu a dalilin tashin hankalin dake ci gaba a yankin.
Fadan da ake a gabashin Ghouta dai ya kara kazancewa a 'yan makonnin nan, yayin da gwamnatin Syria da goyon bayan dakarun Rasha suka 'kara kaimin ganin sun sake kwato yankunan da ake kwace tun shekarar 2013.
Kusan makonni biyu da suka gabata kwamitin sulhu na MDD ya nemi a dakatar da fadan da ake a duk fadin Syria har na tsawon kwanaki 30, domin samar da abinci da kayayyakin agaji ga wadanda suke bukata, amma anyi burus da wannan bukata.
Facebook Forum