Yayin da yake jawabi a taron bitar, babban hafsan hafsohin mayakan sama Air Mashal Sadiq Abubakar, ya ce samar da rahotannin tsaro abu ne mai matukar muhimmanci don ci gaban ‘kasa a wannan lokaci, kuma ta hanyar da ake sarrafa shi ta sigar labarai ka iya shafar sha’anin tsaron kasar ta hanyar da zai yiwa kasa kyau ko kuma ya illa.
Taron bitar ya nuni da cewa dole ‘yan jaridun dake hada rahotannin tsaro su fahimci muhimman al’amuran dake tattare da bangaren tsaro, don basu damar gudanar da ayyukansu bisa tsari da kwarewa.
Tun da farko cikin jawabinsa kakakin rundunar sojan saman Najeriya, Olatokunbo Adesanya, ya ce makasudin wannan taron bitar shine ana son samar da kwarewa ta musamman ga ‘yan jaridun dake dauko rahotannin tsaro.
Rundunar sojan saman Najeriya ta yi fatan cewa ‘yan jaridu ba zasu bari ‘yan ta’adda su yi amfani da su ba, ta hanyar yada profaganda. Yayin taron an ilimantar da ‘yan jaridu kan nau’o’in jiragen yakin Najeriya da ire-iren makaman rundunar sojan saman kasar, har ma da shirye-shiryen da ake kafin akai kowanne irin hari.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum