A sanarwar hadin gwiwar da kungiyoyin suka fitar sun fara da tunatar da jama’a cewa kasar Nijar babu abin da take bukata, illa bullo da matakan kare martaba da mutuncin kasa a idon duniya.
Haka kuma wajibi ne gare su su kasance masu jajirce wa akan maganar hadin kan jama’a ba cece-ku-ce ba.
Zanga-zangar kin jinin gwamnati a dalilin sabuwar dokar harajin 2018 da zanga-zangar masu goyon bayan hukumomi ke shirya wa domin mayar da martani ba za su kai ga samar da maslaha ba.
Dalilin haka saboda haka kungiyoyin Islama ke gargadin bangarorin a kai.
A cewar kakakin kungiyoyin addinin Islama, Sheik Shuaibu Mohamman, ‘yancin dan kasa da hakkin da suka rataya a wuyansa ba wai tsarin mulkin kasa kawai ne ya umarci jama’a da mutuntawa ba, hatta addini ma ya yi gargadi akan wannan kyakkyawar dabi’a.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Sule Muminu Barma.
Facebook Forum