A cewar gwamna Lalong, ganin yadda shugaban Najeriya ya mayar da hankali wajen habaka harkar noma a kasar, hakan yasa gwamnatinsa itama ta yi yunkurin taimakawa namoma inda ta sayi motocin noma da akae kira tarkta har 400.
Gwamnan ya kuma zaga da ‘yan jaridu domin ganin wasu ayyukan da shugaban kasa Mohammadu Buhari zai kaddamar a gobe, wanda suka hada da hanyar mararrabar jama’a wanda take karkashin gwamnatin tarayya.
Shugaban kungiyar manoman jihar Filato Mista Joshua Betrice, ya bayyana jin dadinsu da kokarin da gwamnati ta bangaren aikin Noma. Wanda ke cewa wadannan taraktocin da aka samar zasu taimakawa manoma wajen gudanar da ayyukansu.
A halin da ake ciki kuma, gwamnatin jihar Filato ta sanar da gobe Alhamis a matsayin ranar hutu don taryar shugaban kasa Mohammadu Buhari.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Zainab Babaji.
Facebook Forum