Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Yanke Hukuncin Daurin Shekaru 14 Ga Jolly Nyame


TARABA: Kofar shiga filin wasan Jolly Nyame dake Jalingo
TARABA: Kofar shiga filin wasan Jolly Nyame dake Jalingo

Babbar kotun birnin tarayya ta yanke hukuncin daurin shekaru 14 ba tare da zabin biyan tara ba ga tsohon gwamnan jihar Taraba Reverend Jolly Nyame

Kotun wacce ke karkashin jagorancin mai shari'a Adebukola Banjoko ta sami tsohon gwamnan da laifi dumu dumu na zamba cikin aminci na zunzurutun kudi har Naira Biliyan daya da miliyan sittin da hudu a karar da hukumar yaki da cin hanci ta Najeriya wato EFCC ta gabatar.

Mr Jolly Nyame wanda ya jagorancin jihar Taraba daga 1999 zuwa 2007 an tuhumeshi da laifukan zamba cikin amici da ha'inci da cin amana da babakere da dukiyar jama'a dama karin wasu tuhume tuhume har 41 inda kotun ta tabbatar masa da laifukan 27 wadda kuma ta tura shi gidan wakafi.

Bisa yadda aka yanke hukuncin, tsohon gwamnan Nyame na da ikon daga ‘kara zuwa kotun daukaka ‘kara harma zuwa ga kotun koli in bai yarda da hukuncin kotun ba.

Facebook Forum

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG