Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ebola Na Barazana Ga Lafiya Da Walwalar Kananan Yara - UNICEF


Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF yayi gargadin cewa barkewar cutar Ebola a jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo na barazana ga lafiya da walwalar yara, haka kuma dole ne a dauki matakai na musamman don taimakawa rayuwar yaran.

Kananan yara a yankunan da cutar Ebola ta shafa a jamhuriyar Congo na fuskantar barazana. Na farko itace ta rayuwa. Ebola cuta ce da ake iya kamuwa da ita cikin sauki, kuma tana kashe kashi 20 zuwa 90 na mutanen da suka kamu da ita.

Asusun tallafawa kananan yara na UNICEF na tunkarar matsalar ne ta hanyar saka al’umma yaki da kwayar cutar. Mai magana da yawun Asusun tallafawa Kannan yara, Christophe Boulierac, ya ce makarantu sune muhimman wuraren da za a iya rage yaduwar cutar ga kananan yara.

Ya ce “Asusun UNICEF na auna hanyoyin kariya a makarantun dake a baki ‘daya yankuna uku dake fama da cutar. Cikin hanyoyin har da kokarin da ake yanzu haka na samar da wuraren wanke hannu a makarantu 277, da kuma goyon bayan kara kaimin wayar da kai da zai kai ga sama da kananan yara 13,000 a biranen Mbandaka da Bikoro da kuma Iboko.”

Barkewar annobar Ebola ta baya da aka gani a Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo da kuma yaduwar cutar a wasu kasashen yammacin Afirka, ya nuna mummunan halin da kananan yara suka shiga ta hanyar rasa iyaye da ‘yan uwansu. Boulierac ya fadawa Muryar Amurka cewa yara marayu na fuskantar wariya saboda alakarsu da cutar.

Boulierac ya ce Asusun UNICEF na daukar matakan kariya. Ya ce kwararru na taimakawa iyalan da annobar Ebola ta shafa. Haka kuma suna taimakawa kananan yaran da suke cikin damuwar rasa wasu na kusa da su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG