Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Majalisar Wakilai Ya Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP


Hon. Adams Jagaba
Hon. Adams Jagaba

Dan Majalisar Wakilai dake wakiltar mazabar Kachia da Kagarko, Adams Jagaba, ya sauya sheka daga jam’iyya mai mulki zuwa jam’iyyar adamawa ta PDP.

Adams Jagaba ya bayyana cewa rashin adalci da ci gaba da dakatarwa daga jam’iyyar ta APC sune dalilan da suka sa ya yanke shawarar komawa jam’iyyar adawa ta PDP.

Da yake magana da Muryar Amurka Adams ya bayyana cewa shi yaje Majalisa ne domin yiwa mutanen da yake wakilta aiki.

Yanzu haka a hukumance Adams Jagaba shine dan majalisar wakilai na farko da ya sauya sheka daga jam’iyyar mai mulki zuwa jam’iyyar adawa.

Domin karin bayani saurari hirar Adams Jagaba da Alheri Grace Abdu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:19 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG