Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Na Farin Ciki Kan Dokar Rage Shekarun Tsayawa Takara


‘Yan kungiyar matasan nan ta ‘NOT TOO YOUNG TO RUN’
‘Yan kungiyar matasan nan ta ‘NOT TOO YOUNG TO RUN’

Matasa a Najeriya sun fara bayyana farin ciki dangane da alkawarin shugaba Muhammadu Buhari na sanya hannu akan dokar rage shekarun tsayawa takarar zabe a kasar domin baiwa matasan damar shiga a dama dasu a fagen siyasar kasar.

Sai dai masana kimiyya na cewa, abu ne mawuyaci dokar rage shekarun tsayawa takarar zaben ta yi tasirin da ake bukata.

Dokar wadda ke cikin jerin dokoki fiye 10 da Majalisar dokoki ta kasa ta mikawa shugaban domin rattaba hannu, ta rage mafi karancin shekarun dantakar shugaban kasa daga 40 zuwa 35 dan takarar gwamna daga shekaru 35 zuwa 30 yayin da mafi karancin shekarun dan takarar Majalisar dokoki ta kasa dana jihohi zai kasance 25.

Yanzu haka dai matasan na bayyana farin ciki dangane da wannan alkawari na shugaba Buhari na sanya hannu akan wannan doka, Kwamrad Kabiru Sa’idu Dakata, na daga cikin matasan da sukayi gangami a kwanakin baya domin matsa lamba domin ganin shugaba Buhari ya sanya hannu akan wannan doka.

Tuni dai masana kimiyyar siyasa ke fashin baki game da tasiri da wannan doka ka iya yi a tsarin siyasa Najeriya ko akasin haka, Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa malami ne a Jami’ar Bayero Kano.

Haka zalika Dr Sa’idu Dukawa ya yi Karin haske dangane da matakan daya kamata a dauka ta yadda matasa ka iya samun damar taka rawa a fagen siyasar Najeriya.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG