Kamfanin Mai na Najeriya NNPC ya kulla wata yarjejeniya da wasu Bankuna na kasashen waje, da zata taimaka wajen inganta harkokin Man fetur da iskar Gas da kasar ke da su.
Manoman shinkafa a jihohin Kano da Jigawa da Katsina sun koka game da tsarin bada lamanin kayan noma karkashin shirin gwamnatin tarayya na tallafawa manoma karkashin kulawar babban bankin Najeriya.
A jamhuriyar Nijar matasan kirista na Majami’ar Evangelique sun fara gudanar da taronsu na kasa karo na 45 a birnin Yamai
A bana maniyata 50,000 ne za su yi aikin Hajjin bana, sabanin dubu chasa'in da biyar, kuma tuni har an riga an kwashe alhazai dubu goma sha daya da dari hudu, wadanda a bana suna sauka a birnin Madina ne kai tsaye.
Masu rajin kare demokaradiya a jamhuriyar Nijar sun maida martani bayan da shugaban kasa Mahamadou Issouhou ya dora alhakin koma bayan ilimi a wuyan dalibai da malaman kasar.
Hukumar NAFDAC mai kula da inganci abinci da magunguna ta Najeriya ta kama kwalaben magungunan tari kimanin miliyan biyu da rabi, bayan da gwamnati ta haramta sayar da duk magungunan tari dake dauke da sinadarin Codeine.
Jakadan Najeriya a kasar Afirka ta Kudu ambasada Ahmad Musa Ibeto ya yi murabus daga aiki, sannan ya fice daga Jam’iyyar APC mai mulki a ya koma jam’iyar adawa ta PDP.
Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya sanar da cewa ya sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.
Babban ‘dan kasuwa kuma attajiri a fadin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya ginawa jami’ar Ibadan makarantar koyon ilimin harkar kasuwanci wadda ta lashe kudi sama da Naira miliyan 400.
Cikin makon nan ne kamfanin sadarwa na Google ya kaddamar cibiyar shirin ba da data kyauta a Najeriya, karkashin wani tsari da ake yiwa lakabi da 200 Wi-Fi hotspots.
Kasar Amurka ta ce a shirye ta ke domin bayar da gudunmawar hadin gwiwa da Najeriya don shawo kan tashin hankalin dake faruwa a jihar Zamfara.
Yayin da ya rage ‘kasa da watanni bakwai a gudanar da babban zabe a Najeriya, hada hadar harkokin siyasa sun fara kankama, ta hanyar gudanar da tarukan magoya baya da kuma neman kuri’ar zaben cikin gida na fitar da gwani.
Rundunar sojojin saman Najeriya ta ce sojojinta sun budewa wasu mayakan kungiyar Boko Haram wuta ta sama a jihar Borno.
Kungiyoyin fafutikar ‘yanci bil’adama a Najeriya sunce jinkirin tafiyar shari’u a kotuna na daga cikin kalubalen da suke fuskanta wajen gudanar da ayyukan su.
Gwamnatin jihar Neja ta bayyana cewar tana tabka asarar kudi kimanin Naira miliyan 200 a duk kowane karshen wata a sakamakon Ma’aikatan Bogi da sukayi katutu a jihar.
Babban bankin duniya tare da hadin gwiwar mahukuntan Najeriya sun bullo da wani shirin tallafawa ‘yan gudun hijirar dake Arewa maso Gabashin Najeriya.
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kasuwar kauyen Karakai dake karamar hukumar Bundugu ta jihar Zamfara, inda suka kashe mutane biyu tare da jikkata wasu da dama
Kasar Netherlands za ta taimakawa Najeriya wajen farfado da tafkin Chadi da kuma dakile sauran ta’addancin da kungiyar Boko Haram ke yi a arewacin kasar.
Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ware duk ranar 18 ga watan Yuli a matsayin ranar tunawa da Nelson Mandela, shugaban Afirka ta Kudu kuma wanda yayi rajin neman ‘yancin bakaken fata.
Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC Dakta Kayode Fayemi, ya lashe zaben jihar Ekiti da aka gudanar ranar Asabar.
Domin Kari