Shirin wanda aka kaddamar a jihar Lagos, ya shigar da Najeriya cikin jerin kasashen duniya hudu masu cin gajiyar tsarin na kamfanin Google, amma ta farko a nahiyar Afrika.
Manufar tsarin dai shi ne saukaka yanayin karba ko aika sakonni ta kafar sadarwar intanet a tsakanin ‘yan Najeriya, musamman dalibai, ma’aikatan harkokin yada labarai masu bincike da kuma ‘yan kasuwa da sauran ma’abota amfani da kafar sadarwar intanet.
Baya ga aikawa da karbar sako cikin sauki da kuma rahusa, masu kula da al’amura na ganin matakin na kamfanin Google na ba da data kyauta wani kalubale ne ga kamfanonin sadarwa a Najeriya wadanda aka dade ana korafi kan rashin ingancin ayyukansu.
Gabanin kaddamar da tsarin na ba da data kyauta ga masu amfani da Intanet, kamfanin da Google ya kaddamar da irin wannan tsari a kasashen India, Indonesia, Mexico da kuma Thailand.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.
Facebook Forum