A Najeriya ana ci gaba da tafka muhawara dangane da canza shugabannin rundunonin tsaro na kasar musamman duba da yadda matsalar tsaron kasar ke Kara daukar wani sabon salo.
Rahotanni daga jihar Ekiti na nuni da cewa yanzu haka an fara kidayar kuri’u na zaben gwamnan jihar da ake gudanrwa.
Gwamnatin Najeriya ta yi karin haske kan dalilan da ya sa taki sakin tsohon mai bada shawara kan harkokin tsaron kasar, Kanar Sambo Dasuki
Ana ci gaba da samun kwararar ‘yan gudun hijira biyo bayan wasu hare-haren da aka kaiwa wasu kauyukan Fulani a karamar hukumar Lau cikin jihar Taraba.
An kamala wani taron kasa da kasa domin inganta adabin baka na yankin nahiyar afrika, taron da kungiyar raya adabin baka ta duniya ta dauki nauyin gudanar dashi a birnin Lagos.
Kokarin da kungiyar raya kasashen ketare da gwamnatin Amurka ke yi na tallafawa Najeriya ta zama mai dogaro da kai ta fuskar abinci, hukumar USAID ta shirya taron bita ga wasu malaman bangaren noma na jami’oin Najeriya domin samun nasarar shirin.
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari garin Tabanni dake yankin karamar hukumar Rabah dake jihar Sokoto, inda suka kashe mutane masu yawa tare da raunata wasu da dama.
Ciki da Gaskiya Wuka Bata Hudashi
Mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed, ta fara ziyara a Jamhuriyar Nijar, domin tattauna hanyoyin magance matsalolin mata a fannoni da dama kamar batun auren wuri da rashin baiwa mata dama a harkokin siyasa.
Rundunar sojojin Najeriya ta yi ‘karin haske kan abin da ya sa ‘yan kungiyar Boko Haram ke sace fararen hula su yi garkuwa da su.
Dan shugaban kungiyar IS Abu Bakir al-Bagdadi ya mutu a wani harin kunar bakin wake da ya kai a birnin Homs a yammacin Syria, bisa ga cewar kafar labaran IS al-Nashir.
Amurka tana bukin zagayowar ranar samun yancin kai a yau Laraba.
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen Bom dake kan iyakar kananan hukumomin Barikin Ladi da Mangu, kusa da marabar Kantoma inda suka kashe mutane shida.
Babbar kotun birnin tarayya Abuja ta wanke babban Hafsa mai kula da harkokin mulki na hedkwatar rundunar sojojin saman Najeriya Air vice Marshall Alkali Mamu.
Kungiyar gwamnonin Najeriya ta ce zata zauna da dukkanin jami’an tsaron kasar don bayyana musu matsalolin tsaro da ake fuskanta a kasar da nufin kawo karshensu
Rundunar tsaro ta musamman a jihar Filato ta ta cafke mutane 17 ake zargi da haddasa rikicin jihar da yayi sanadiyar rasa rayuka.
An yi ganawa ta musamman a fadar gwamnatin tarayya tsakanin shugaban Najeriya da shugabannin Majalisun ‘kasa.
Jam’iyya mai mulki a Najeriya APC ta kammala babban taron da ta yi a Abuja inda ta sake zabar sabbin shugabaniin da zasu gudanar da al’amuran jam’iyyar.
Domin Kari