Shugaban Hukumar kula da harkokin ma’aikata a jihar Neja, Alhaji shehu Galadima, ya ce matsalar cuwa-cuwa a bangaren ma’aikatan gwamnati na karuwa. Ya kuma bayyana cewa yanzu haka wata kotu ta samu wasu ma’aikata biyu da laifin buga takardun bogi, wadanda aka yanke musu hukuncin daurin shekaru takwas a gidan Yari.
Kungiyar kwadagon jihar Neja ta tabbatar da cewa ta bankado kimanin ma’aikatan bogi dubu a lokacin da gwamnan jihar ya sa su cikin wani kwamitin tantance ma’aikatan bogi da har yanzu ba a bayyana rahotonsa ba.
Shugaban kungiyar kwadago kwamarad Yahaya Idris Ndako, ya ce anasu binciken gwamnatin jihar Neja na asarar kimanin Naira Miliyan 266 a duk karshen wata a sakamakon ma’aikatan bogi.
Wannan bayani dai yayi matukar tayar da hankalin jama’a a jihar ta Neja, Alhaji Umma kolo, dake zaman daraktan harkokin matasa ya ce lamarin na da tayar da hankali dan haka akwai bukatar daukar mataki.
Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.
Facebook Forum