Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya : Wasu Manoman Shinkafa Sun Koka Kan Tallafin Da Gwamnati Ta Basu


Gonar shinkafa
Gonar shinkafa

Manoman shinkafa a jihohin Kano da Jigawa da Katsina sun koka game da tsarin bada lamanin kayan noma karkashin shirin gwamnatin tarayya na tallafawa manoma karkashin kulawar babban bankin Najeriya.

Tun a shekara ta 2016 ne gwamnati Najeriya ta kaddamar da wannan shiri da nufin bunkasa noman shinkafa a karkashin tsarin ta na dakile shigo da shinkafa cikin kasar daga ketare.

Alhaji Yakubu Tagahu, dake zama manomin shinkafa daga yankin karamar hukumar Takai a jihar Kano, ya ce har ya zuwa yanzu akwai sauran kayayyakin aiki da ba a basu ba. Haka kuma an baiwa mutane kayan cikin karancin lokaci.

Haka kuma an baiwa manoman kayayyakin ne kan kudaden da suka ninka wanda ake sayar da su yanzu haka a kasuwa.

Shi kuwa Malam Husssaini Dutse daga jihar Jigawa cewa yayi wannan ba taimako bane domin kuwa kamar anyi kasuwanci da su ne, idan aka yi la’akari da kudaden da kungiyar ta sayar musu da kayan.

Alhaji Rabe Yusuf guda cikin manoman da suka karbi bashi karkashin wannan tsari na bada lamanin noman shinkafa, cewa yayi yanzu haka basu san halin da ake ciki ba, domin kuwa basu da masaniyar ko akan wane farashi aka basu ba.

Sai dai sakataren kungiyar manoman Shinkafa ta Najeriya, RIFAN dake zaman jakadiyar bankin kasa na CBN ta hanyar rarraba wadannan kayayyaki ga manoman.

Alhaji Ado Hassan Yakasai dake zama mataimakin sakataren kungiyar manoman shinkafa ta kasa reshen jihar Kano, ya bayyana cewa a zahiri babu wani kayan da aka daura masa kudin da ya wuce hankali.

Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG