Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kananan Yaran Dake Zaune a Kasashen Da Ebola Ta Afkawa Sun Koma Makarantunsu


Asusun tallafawa kananan yara na MDD UNICEF -ya bada rahoto cewa, galibin yara da suke zaune a yankunan da aka sami bullar cutar Ebola a Damokaradiyar Jamhuriyar Congo sun koma makaranta, inda aka koya masu yadda zasu kare kansu daga kamuwa da cutar.

An bude makarantu a Damokaradiyar Jamhuriyar Congo ne watan da ya gabata. Asusun UNICEF yace an sami gagarumar nasara a kokarin ganin yara sun koma makaranta a yankin da aka yi fama da cutar ta Ebola.

Kakakin asusun Christophe Boulierac yace, sun sami kwarin guiwa sosai ganin yara da dama sun koma makaranta. Yace makaranta tana samar da yanayi da ya dace.

Bourlierac yace yaran da suke makaranta suna koyon yadda zasu kare kansu daga kamuwa da Ebola idan sun koma gida. Yace wannan yana taimakawa wajen dakile yada cutar a tsakanin al’umma.

Asusun UNICEF ya kirga sama da makarantu dubu daya da dari biyar a yankunan da aka sami bullar cutar Ebola. Daga cikinsu, makarantu dari uku da sittin da biyar suna inda cutar tafi barazana. Cibiyar ta samar da makayan kiwon lafiya da tsabtace muhalli a wadannan makarantun.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG