Kungiyar Civilian JTF dai na aikin farauta ‘yan kungiyar Boko Haram a jihar Borno. An dai kirkiro kungiyar aikin sa kan ce a lokacin da ‘yan kungiyar Boko Haram suka fara addabar al’ummar garin Maiduguri.
Sai dai tun lokacin da aka kirkiri kungiyar a ba tantance shekarun matasan da zasu iya yin aiki da kunigiyar ba. a baya-bayan nan ne aka shiga wata yarjejeniya da Asusun tallafawa yara na MDD da ake kira UNICEF da kuma gwamnatin jihar Borno.
Yanzu haka dai an kebe yaran da shekarunsu yayi kasa da 18, aka sallamesu daga cikin kungiyar CJTF. Jakadan Amurka Mr. Stuart Symington, ya ja hankalin matasan da aka sallama ta hanyar basu shawarar yin tunannin ilimi da kiwon lafiya da kuma yadda rayuwarsu za ta kasance.
Barista Abdullahi Hussaini Isge, na ma’aikatar shari’a dake jihar Borno, ya ce a cikin wannan tafiyar an rasa jami’an CJTF 809, sannan kuma yanzu haka sun kebe matasa ‘yan kasa da shekaru 18 su 833 haka kuma wasu guda 3,701 sun mikawa Asusun tallafawa kananan yara UNICEF.
Wakiliyar UNICEF a Najeriya ta ce yanzu haka sun karbi matasan, haka kuma zasu tabbatar da ganin cewa matasan sun koma makaranta sun ci gaba da karatunsu.
Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda.
Facebook Forum