Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sudan Na Kuka Game Rage Darajar Kudin Kasarsu


Kudin kasar Sudan
Kudin kasar Sudan

Da yawan ‘yan kasar Sudan suna kokawa game da yadda gwamnatin Sudan din ta sake rage darajar kudin kasarta ranar Lahadi, da kusan rabi, yayin da tattalin arzikin kasar ke cikin halin kaka-ni-kayi.

Kawo karshen dadadden takunkumin tattalin arzikin da Amurka ta sakawa Sudan a shekarar 2017, bai haifar da fatan da ake na farfado da tattalin arzikin kasar ba, kuma Sudan ta kasance cikin jerin sunayen kasashen da Amurka ke dauka a matsayin masu tallafawa ta’addanci a duniya.

Bayan da gwamnatin kasar ta rage darajar kudin kasar daga 28 zuwa 47.5 kan kowacce dala. Wasu mata da ke sayayya a wata kasuwar kayan gwari a babban birnin Khartoum, sunce farashi ya ‘karu, kuma hauhawar farashin kayayyaki ya kai kashi 70 cikin 100 tun farkon wannan shekara.

Sabon Fara Ministan Sudan da aka nada Moataz Moussa ya fadawa ‘yan Majalisu ranar Litinin cewa, gwamnati ba zata yi komai kan daidaituwar kudin kasar ba.

“Ya ce babu tabbacin abin da za a yiwa kudin Sudan darajarsa ta daidaita da Dala.”

Masana tattalin arziki a Sudan na kyautata zaton tattalin arziki zai farfado bayan da Amurka ta janye takunkumin tattalin arziki na kusan shekaru 20 a shekarar da ta gabata, amma yin hakan bai taimaka ba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG