“Akwai bambanci tsakanin kwayar hatsi da iri, shi iri ba a sayar da shi a budedden masaki, sai a rufaffe kuma da rubutu a jikin shudiyar takar da da ke nuna cewa wannan iri ne” Inji shugaban hukumar bunkasa iri mai inganci a Najeriya Dr. Olusegun Ojo, a gangamin wayar da kan manoma muhimmancin aiki da iri ba shuka hatsi na abinci ba don samun yabanya.
“kuma ya zama wajibi a samu sunan wanda ya samar da irin don idan an samu wani cikas za ka iya bin sawun mai samar da irin”
Kwararru kan lamuran noma sun alakanta rashin samun yabanya mai kyau da rashin ingancin iri, don a cewar su matukar a ka samu iri mai inganci zai dau kimar takin zamani ya kuma samar da amfanin gona da zai wadaci bukatun manya da kananan manoma.
Hukumar dai na karkashin ma’aikatar gona, kuma akwai irin ta a karkashin hukumomin noman jihohi da kan koyar da dabarun samun iri na gari da tazarar da ta dace a samu tsakanin shuka hakanan da ba da shawari kan yadda za a magance ciyawa ba tare da cutar da shuka ba.
Noma dai shine tushen arzikin Najeriya a zamanin turawa da ya samu koma baya bayan gano man fetur.
Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Facebook Forum