Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya da Chadi Sun Hallaka ‘Yan Boko Haram 124


Sojoji Najeriya kusa da Maiduguri, Mayu 14, 2015.
Sojoji Najeriya kusa da Maiduguri, Mayu 14, 2015.

Jami’an sojan Najeriya da hadin gwiwar na kasar Chadi sun ce sun hallaka ‘yan kungiyar Boko Haram 124 a wasu hare-hare daban-daban da su ka kai musu.

Rundunar sojan Najeriya ta fitar da sanarwa dake cewa, wasu ‘yan Boko Haram 76 sun gamu ajalinsu a lokacin da suke kokarin kai hari akan sansanonin jami’an soja a kauyen Maitale dake garin Kangarwa a arewacin Borno.

Sanarwa ta kara da cewa, sojojin Chadi sun hallaka wasu ‘yan Boko Haram 48, bayan da suka yi kokarin kai wa sansanin sojojinsu hari.

Haka kuma rundunar ta kuma tarwatsa wasu ‘yan Boko Haram su 76, sai dai abin takaici shine rundunar ta rasa wasu jami’anta 7, wasu 17 kuma suka ji rauni. Tuni dai babban hafsan sojan Najeriya Janar Tukur Buratai ya jajantawa iyalan mamatan, ya kuma yi alkawarin basu kulawa da samar da magani ga wadanda suka jikkata.

A daya bangaren kuma, sojojin Chadi guda takwas sun rasa rayukansu, haka kuma an kashe wasu mayakan Boko Haram 48 sakamakon arangamar.

Hare-hare daga mayakan Boko Haram ke kaiwa na ci gaba da daukar hankalin al’ummar dake yankin tafkin Chadi.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Haruna Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:42 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG