Barazanar shiga yajin aikin na zuwa ne daidai lokacin da kotun kula da lamuran aikin gwamnati ta umurci kungiyar kwadago ta dakatar da matakin har sai ta gama sauraron shari'ar da gwamnati ta shigar da wata kungiya mai marawa gwamnati baya.
A taronta na karshe a gidan kwadago da ke Abuja kungiyar NLC da ke samun hadin kan ta kamfanoni TUC, ta ce ba gudu ba ja da baya kan wannan yajin aiki har sai gwamnati ta janye tagwayen karin farashin da ta yi.
Shugaban kungiyar kwadagon Ayuba Wabba ya sha nanata wahalar da ya ce ma'aikata kan shiga sakamakon karin farashin fetur.
Tuni wata kungiya mai marawa janye tallafin fetur baya ta yi gangami a Abuja don gargadin sa kafar wando daya da kungiyar kwadagon ta na mai cewa ai ba yanda ma za a dawo da tallafin na fetur.
"Za mu kalubalanci 'yan kwadagon a kotu kuma in sun fito kan titi za mu yi fito na fito da su..."
In ji jagoran magoya bayan da suka yi taro a Dandalin UNITY.
Gwamnatin baya ta PDP da ta nemi cire tallafin fetur ta samu kalubalen gaske a wajen 2012 inda ala tilas ta ci gaba da ba da tallafin; a lokacin wannan gwamnati na 'yar adawa inda jama'arta suka nuna lalle tallafin na da amfani.
Duk da haka shugaba Buhari bai taba goyon bayan tallafin ba don a mahangarsa hakan wata hanya ce ta almundahana.
Halima Kajuru 'yar jam'iyyar adawa ce da ke tuna abun da ta ce alkawarin zane a kan ruwa na APC.
Dakatar da batun yajin aiki a kotu ba sabon abu ba ne kuma bai taba hana kungiyar kwadago daukar matakinta ba duk da ma ana zargin ita kanta kwadagon da zama dillaliyar gwamnati wajen kara farashin fetur tun da an ga yajin aiki bai taba sa an janye dukkan karin da a ka yi ba a baya.
Facebook Forum