Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kwadagon Najeriya Ta Janye Yajin Aiki


ABUJA: 'Yan kungiyar kwadago masu zanga zanga
ABUJA: 'Yan kungiyar kwadago masu zanga zanga

Kungiyar Kwadagon Najeriya ta NLC da gamayyar kungiyoyin kwadago ta TUC, sun janye yajin aikin gama-gari da suka shirya shiga yau Litinin, 28 ga watan Satumban shekarar 2020, akan karin farashin man fetur da wutar lantarki.

An sami cimma daidaito ne bayan gudanar da wani taro tsakanin gwamnati da wakilan kungiyar kwadago da ya share tsawon lokaci har zuwa karfe biyu na daren Lahadi a agogon Najeriya.

Kungiyar kwadagon ta amince da janye yajin aiki sa'a biyu bayan fara shi don matsawa gwamnati lamba ta dawo da tallafin man fetur ta kuma rage farashin wutar lantarki.

Gwamnatin Najeriya ta APC da ta sha sukar tsohuwar gwamnatin PDP kan karin farashin fetur gabanin lashe zabe a 2015, ta kara farashin litar fetur da kusan kashi 100% da ba a taba samun haka a tarihin gwamnatocin kasar ba tun samun 'yancin kai a shekarar 1960.

Bayanan janye yajin aikin sun nuna gwamnati za ta bullo da wasu shirye-shirye na tallafin rage radadi kamar yanda tsohuwar gwamnatin PDP ta yi, kazalika ta janye karin kudin lantarki na tsawon mako biyu don nazarin matakin da ya fi dacewa.

Mataimakin sakataren hulda da kungiyoyi na kungiyar kwadagon Komred Nasir Kabir ya ce matakin yajin aikin duk da an janye, ya sami nasara tun da akalla gwamnati ta dakatar da karin farashin lantarki.

Komred Kabir ya musanta cewa matsin lamba ya sanya kungiyar kwadagon janye yajin aikin.

A karkashin yarjejeniyar da aka cimma, bangarorin biyu sun amince da kafa kwamitin masana a farashin kundin wutar lantarki da za su hada da wakilai daga ma’aikatun gwamnatin tarayya da wakilan kwadago da zasu yi aiki tsawon makwanni biyu daga yau Litinin domin fito da sabon farashin kundin wuta.

Ministan kasa mai kula da harkokin kwadago, Festus Keyamo, shine zai jagorancin wannan kwamitin na masana da zai yi nazari a kan fito da sabon farashin kudin wutar lantarki.

Ga dai rahoton Nasiru Adamu El Hikaya a kan haka:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Facebook Forum

Zaben 2023

TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Tasirin Da Zaben Donald Trump Zai Yi A Harkokin Kasashen Duniya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG