Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba SARS Kawai Ba, Daukacin Tsarin Aikin ‘Yan Sanda Ke Bukatar Gyara – In Ji Jama’a


'Yan sandan Najeriya
'Yan sandan Najeriya

A cigaba da tattaunawa da 'yan Najeriya ke yi kan matsalar kuntata ma jama'a da 'yan sanda na musamman kan yi, an bukaci a yi garanbawul ma tsarin aikin 'yan sanda gaba daya, ba SARS kawai ba.

A daidai lokacin da jihohi ke tattara bayanai game da korafin jama'a kan yadda rundunar 'yan sandan SARS da a ka rushe ta ci zarafinsu, bukatar ta dada fadada ta yadda a yanzu ta hada da neman yin garambawul ga dukkan sassan 'yan sanda don hana al'adar amfani da kayan sarki wajen cin zali ko danne hakkin 'yan-adam.

A na zargin 'yan sandan na SARS da yanke hukunci da kan kai ga rasa wanda a ke tuhuma ba tare da kai wanda a ke zargin gaban kotu ba. Ga kuma batun hukuncin gwale gwale da wasu ke zargin an yanke masu au cikin kuskure au bisa tsabar zalunci.

A demonstrator holds a placard to protest against abuses by the Special Anti-Robbery Squad (SARS) at the Lekki toll Plaza in Lagos, Nigeria, Oct. 12, 2020.
A demonstrator holds a placard to protest against abuses by the Special Anti-Robbery Squad (SARS) at the Lekki toll Plaza in Lagos, Nigeria, Oct. 12, 2020.

Duk da a na cewa 'yan sandan sun yi karanci in an dubi yawan 'yan Najeriya, amma akan gansu barkatai tare da manyan jami'an gwamnati su na tafiya cikin yanayin da kan yi barazana ga sauran masu amfani da tituna.

Abubakar Shumo wanda ya shiga hannun 'yan SARS a Abuja, ya baiyana yadda hatta gawar da ke lullube da likkafani ba ta tsira daga wuce gona da iri na ‘yan sandan SARS ba.

Marigayi mai kama barayi Alhaji Ali Kwara ya bayyana zamba cikin aminci da wani dan SARS ya yi wanda hakan ke kara tabbatar da cin hanci da rashawa a rusasshiyar rundunar.

Ga 'yan sandan da ba ma na SARS ba, a Bauchi ana jiran sakamakon binciken DPO Baba Ali Muhammed wanda a ka zarga da dukar kawo wuka ga yara 3 har biyu su ka mutu saboda zargin sun yi satar kaza.

Kakakin rundunar a Bauchi, DSP Muhammad Wakili ya ce an kafa kwamitin bincike.

Nigeria Police Protest
Nigeria Police Protest

Ministan 'yan sanda Maigari Dingyadi ya ce sam ba za a amince sabuwar rundunar da ta maye SARS, wato SWAT, ta mallaki jami'ai marasa imani ba.

Da alamu jami'an 'yan sanda masu zafin kai kan tabuka abun kirki a jihohin da ke da kalubalen 'yan ta'adda, amma su kan huce kan farar hula a jihohin da babu barazanar 'yan ta'addan.

Ga Nasiru Adamu Elhikaya da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG