Kungiyar da ta yi taro a Abuja don karfafa zaman lafiya a kudancin Kaduna da kuma jihar Edo da ke shirin zaben gwamna, ta ce son zuciya na kan gaba a lamuran da ke haddasa fitina. A cewarta "ba wani addini da ke koyar da fitina ko ma zubar da jini."
Sakataren kungiyar na gefen Krista Ibrahim Joshua da Alhaji Ibrahim Yahaya na Musulmi sun ce cusawa mutane akidar tsoron Allah zai taimaka ainun wajen sulhunta su da hana su zaman gaba da juna.
Ita ma Lantana Bako Abdullahi, wata 'yar kungiyar na nuna takaicin da zarar an samu fitina, mata ne kan zama mafiya shan wahala.
Tsohon shugaban matasan kungiyar kirista “CAN” Pastor Simon A.S. Dolly ya halarci taron kuma ya ce fitinar addini na da saurin yin illa.
Kungiyar dai na aiki bisa jagoarancin Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar da kuma shugaban kungiyar kirista (CAN) Reverend Olasupo Ayokunle.
Ga Nasiru Adamu Elhikaya da cikakken rahoton:
Facebook Forum