Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sako Daliban Jami'ar Ahmadu Bello Bayan Biyan Kudin Fansa


Wadanda Suka Tsira Daga Masu Satar Mutane a Hanyar Kaduna Zuwa Abuja.
Wadanda Suka Tsira Daga Masu Satar Mutane a Hanyar Kaduna Zuwa Abuja.

Mako daya bayan sace daliban sashen Faransanci na jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria su tara,da wasu mutane da masu satar mutane su ka yi a hanyar Kaduna zuwa Abuja, an samu nasarar sako su bayan biyan kudin fansa.

Daliban dai wadanda ke kan hanyar tafiya cibiyar koyon harshen Faransanci da ke Badagry a Lagos, sun fada komar masu sace mutane ne, inda da farko aka nemi iyayensu, su biya fansar Naira miliyan 30 kan kowane dalibi.

'Yan uwan daliban sun ce sun dage da tattaunawa da masu satar mutanen har ta kai ga daidaitawa kan biyan kudin fansa mai dan rangwami, sakamakon labarin Muryar Amurka da ya fito da batun satar bayan majiyar hukuma ta ce an ceto kowa, da kuma addu'o'in da a ka yi ta yi.

kudin da a ka biya sun kama daga Naira dubu 400 zuwa dubu 700 har sama da miliyan guda kan kowanne dalibi, inda a ka sako daliban a kwanar Abuja da ke yankin Kachia a jihar Kaduna.

Wata 'yar uwar daliban, Alheri Akwachim Musa ta ce duk da haka masu satar sun taba lafiyar daliban sanadiyyar jin labarin da Muryar Amurka ta yada.

Jami'in Hulda da jama'a na jami'ar Ahmadu Bello Auwalu Umar, ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa an sako daliban kuma sun gamu da danginsu duk da bai ambaci ko an biya kudin fansa ba ne ko a'a.

Daya daga 'yan uwan daliban ya nuna matukar damuwa da cewa ba su samu wata gudunmawa da ta taimaka wajen sako daliban ba.

Hanyar Abuja zuwa Kaduna ta zama tarkon sace matafiya da hakan kan sa fasinjoji cika tashar jirgin kasa don samun natsuwa duk da kalubalen samun tikiti da jinkiri.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-hikaya daga birnin Tarayya Abuja:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG