Sahihan bayanai na nuna cewa masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC na daukar matakan karshe don cankar wanda su ke ganin ya dace ya zama dan takararsu a babban zaben 2023, wannan na zuwa ne bayan zabar tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar a matsayin dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP.
Irin wannan hanya za ta bullo da hanyoyin samun kudi ba da dogaro kacokan ga kudin da jihohin kan samu a wata daga gwamnatin taraiya ba.
Jam’iyyar APC mai mulki a tarayyar Najeriya na shirin gudanar da zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa da ‘yan takara 23.
Tsohon sakataren gwamnatin Najeriya Babachir David Lawal ya ce sai 'yan arewa sun kaunaci juna ta hanyar kaucewa bambancin kabilanci za su samu dawo da tagomashin yankin kwatankwacin yanda ya ke a Jamhuriya ta farko.
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya lashe tikitin zaben shugabancin Najeriya a inuwar jam’iyyar PDP.
Shirin har ila yau ya tabo batun matsalar makiyaya da manoma a yankin karamar hukumar Jama'a da ke kudancin jihar Kaduna a Najeriya.
APC ta jaddada cewa za ta gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa a inuwar jam'iyyar ranar lahadi 29 ga watan nan.
‘Yan takarar shugaban kasa na manyan jam’iyyu na cigaba da zaga jihohin da musamman su ke da yawan wakilai don neman goyon baya a zaben fidda gwani.
Masu sharhi sun ce bude tashosin zai samar da ayyukan yi ga matasa a yankin na arewacin Najeriya da ba shi da iyaka da teku.
Manyan lauyoyi a Najeriya sun shiga bayyana mabambantan ra’ayoyi kan dacewar sake takarar tsohon Shugaba Kasa Goodluck Jonathan, bayan da wata gamayya mai da’awar ta arewa ce ta saya ma sa fom din APC na takara kan Naira miliyan 100.
Dandazon ‘yan Najeriya da su ka kammala a umrah, sun makale a filin jirage na Jiddah bayan sun sami cikas din jirgin da zai dawo da su.
Dattawan jam’iyyar PDP na arewa sun yi taron gaggawa a Abuja inda su ka nuna rashin amincewa da duk wani taro da ke nuna fitar da dan takara daya daga arewa gabanin fidda gwani.
A ci gaba da takaddamar da ake yi kan batun tsayar da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP ba tare da zaben fitar da gwani ba, jam'iyyar ta fito fili ta yi watsi da batun tsayar da dan takara ta hanyar sulhu.
Jam’iyar PDP ta bayyana cewa a yanzu haka ta na da ‘yan takarar shugaban kasa 17 daga arewa da kudancin Najeriya da ta ke sa ran shiga zaben fidda gwani da su.
‘Yan Najeriya sun shiga muhawara biyo bayan sanarwar majalisar koli ta APC ta sayar da fom din shiga zaben fidda gwani a inuwar jam'iyyar kan Naira miliyan 100.
Gwamnoni na ci gaba da daukar matakai don xjuya akalar babban zaben Najeriya a shekarar 2023.
Gwamnoni na cigaba da daukar matakai don taka rawar juya akalar babban zaben Najeriya a 2023.
Domin Kari