Mataimakin shugaban jam’iyyar na arewacin Najeriya Ambasada Umar Iliya Damagum ya bayyana haka a lokacin da ya ke amsa tambaya kan zaman daidaitawa tsakanin ‘yan takara 4 na arewa da Janar Babangida ya jagoranta.
A taron sulhun dai da gwamnan Bauchi Bala Muhammad da tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki su ka yi nasara, bai samu sanya hannun gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal ba, inda tun farko ma Atiku Abubakar bai shiga sulhun ba
Ambasada Damagum ya ce ‘yan takarar na da hurumin bin dabarun su na hulda da juna, amma ba a karkashin jam’iyya ko tsarin ta a ka gudanar da taron mutum hudun ba, da ta kai ga kungiyar dattawan arewa karkashin farfesa Ango Abdullahi da sauran dattawa kada kuri’a.
Gwamna Bala Muhammad ya ce koma me za a ce ba shi da wata rashin jituwa da sauran ‘yan takara musamman ma gwamna Tambuwal.
A bangaren kungiyar dattawan arewa, darakta a kungiyar Dr.Sadiq Umar Gombe ya ce sulhun shi ya fi wa arewa a’ala.
Alamu dai sun nuna PDP za ta tafi zaben fidda gwani da dukkan ‘yan takarar ta, a tsarin ta na yanzu da ya bar kofar takara a bude ga kowa.
Saurari cikakken shirin cikin sauti: