Fasinjojin wadanda kamfanin jirgin Max mallakar Dahiru Barau Mangal ya yi jigalarsu suna nuna bukatar daukin gaggawa don wasun su, guzurin su ya kare.
Bayanai na nuni da cewa, da farko an jibge fasinjojin a sashen tashin jirage na kasa da kasa a Jidda inda don yawan su ala tilas Saudiyya ta sauya mu su matsuguni zuwa sashen sauka da tashin alhazai MADINATUL HUJJAJ inda ke da ‘yan wajajen runtsawa.
Alhaji Ibrahim Hamza da ke cikin fasinjojin ya ce bayan hatsaniya, hukumomin filin jirgin sun dauke su, su ka kama mu su masaukai a daf da filin.
Kakakin kamfanin jiragen na Max Ibrahim Dahiru ya ce kamfanin ya riga ya dawo da wasu fasinjojin kuma ba lalle ne akwai wani sakaci daga bangaren sa kan halin da ‘yan umrar su ka shiga ba.
Yayin da raderadi ke nuna Saudiyya ta dakatar da jigilar ‘yan umrar na Najeriya na wani dan lokaci, fasinjoji sun ce wasu jiragen na tashi zuwa Najeriya ta jirgin Saudi wato Saudi Air.
Saurari rahoton Nasiru Adamu El-hikaya cikin sauti