Yayin da ake ta takaddama game da wani zaman sulhu tsakanin Gwamna Bala Mohammed na jahar Bauchi, da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jahar Sokoto, da tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Bukola Sarki, da kuma Alhaji Mohammed Hayatuddeen, wanda a karshe ya kai ga cewa an tsayar da Gwamna Bala Mohammed, amma Gwamna Tambuwal ya ce ba
Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa a yanzu haka ta na da ‘yan takarar shugaban kasa 17 daga arewa da kudancin Najeriya wadanda ta ke sa ran za su shiga zaben fidda gwani.
Mataimakin shugaban jam’iyyar na arewacin Najeriya, Ambasada Umar Iliya Damagum, ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke amsa tambaya kan zaman daidaitawa tsakanin ‘yan takara 4 na arewa da tsohon Shugaban Kasa, Janar Ibrahim Babangida (murabus) ya jagoranta.
A taron sulhun dai da gwamnan Bauchi, Bala Muhammad da tsohon shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki su ka yi nasara, bai samu sanya hannun gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal ba, inda tun farko ma tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar bai shiga sulhun ba.
Ambasada Damagum ya ce ‘yan takarar na da hurumin bin dabarunsu na hulda da juna, amma ba a karkashin jam’iyya ko tsarin ta aka gudanar da taron mutum hudun ba, da ta kai ga kungiyar dattawan arewa, karkashin farfesa Ango Abdullahi da sauran dattawa kada kuri’a.
Gwamna Bala Muhammad ya ce koma me za a ce ba shi da wata rashin jituwa da sauran ‘yan takara musamman ma gwamna Tambuwal.
A bangaren kungiyar dattawan arewa, darakta a kungiyar, Dr.Sadiq Umar Gombe, ya ce sulhun shi ya fi wa arewa a’ala.
Alamu dai sun nuna PDP za ta gudanar da zaben fidda gwani ga dukkan ‘yan takararta, a tsarin ta na yanzu da ya bar kofar takara a bude ga kowa.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Elhikaya: