Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Ni Na Yi Maganganun Da Aka Karrada A Kafafen Sadarwa Ba-Babachir


Babachir David Lawal
Babachir David Lawal

Tsohon sakataren gwamnatin Najeriya Babachir David Lawal ya ce sai 'yan arewa sun kaunaci juna ta hanyar kaucewa bambancin kabilanci za su samu dawo da tagomashin yankin kwatankwacin yanda ya ke a Jamhuriya ta farko.

Babachir Lawal na magana ne kan tabarbarewar tsaro da zargin juna da ya ce ya na damun hadin kan arewa.

Tsohon sakataren wanda a 'yan kwanakin nan a ka yada wani sauti na neman tada fitinar addini da aka ce shi ya yi maganar alhali ba shi ba ne, ya bukaci dattawa a arewa su tashi tsaye wajen rage yawan fahimtar juna.

Lawal ya ce ba inda ya kai arewa albarka, amma a na samun kalubalen rikicin cikin gida tsakanin al'ummar yankin.

Tsohon sakataren ya ce a matsayin sa na mai bishara, ya ce ya yi imani ba addinin da ya haramta kisan gilla ba tare da hakkin shari'a ba.

Shugaban samarin karamar hukumar Jama'a a jihar Kaduna Alhaji Mudi Shafi’u Tahir inda asalin wanda ya fitar da sautin ya fito; ya ce an sha yi wa mutumin gargadi dangane da illar wannan dabi'ar, ya kuma ce mutumin ba shi da goyon bayan akasarin al'umma.

Yankin arewa na da kalubalen rashin jituwa ta fuskar addini da bambancin kabilanci da kan zama sanadiyyar fitina a wasu yankuna, da ya zama mai muhimmanci magabata ke karfafa kaucewa furta kalaman batanci da biyewa kabilanci.

Sauri cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

XS
SM
MD
LG