Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tasirin Naira Miliyan 100 Kudin Fom A Tsaida Dan Takarar Jam'iyar APC


Taron majalisar zartarwar gwamnatin Buhari a Najeriya. (Hoto: Fadar shugaban kasa)
Taron majalisar zartarwar gwamnatin Buhari a Najeriya. (Hoto: Fadar shugaban kasa)

‘Yan Najeriya sun shiga muhawara biyo bayan sanarwar majalisar koli ta APC ta sayar da fom din shiga zaben fidda gwani a inuwar jam'iyyar kan Naira miliyan 100.

ABUJA, NIGERIA - Hakan ya sa akasarin mutane na ganin jam'iyyar ta sauya daga ta talakawa ta koma ta 'yan jari hujja.

Duk da manyan 'yan takara na da nauyin aljihun da za su sayi fom din ko ma wasu 'yan baranda su ce sun saya mu su, hakan ya rufe damar tsayawar ga wanda ba shi da miliyoyi ko da ya canacanta.

Duk da wannan fargabar ta nuna jam'iyyar ta sauka daga yanda shugaba Buhari ya samu nasara da gudunmawar talakawa, mai taimakawa shugaban kan labaru Garba Shehu ya ce APC za ta kai labari.

Ba haka tsohon gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso ke gani ba musamman bayan ya yi bankwana da APC da PDP ya shiga karamar jam'iyyar adawa ta NNPP.

Masu sharhi kan lamura sun bayyana cewa, ba kudin sayan fom din ne abin damuwa ba, yadda za a kula da walwalar wakilan da za su zabi dan takara shi ne wata maganar.

Saurari rahoto cikin sauti daga Nasiru Adamu El-Hikaya:

Mahawara Ta Barke A Najeriya Game Da Kudin Fom Din Naira Miliyan 100 Na Shiga Takarar Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG