Taron da ya hada tsoffin gwamnonin jam’iyyar PDP ya gudana karkashin jagorancin tsohon gwamnan Jigawa Sule Lamido da tsohon minister Adamu Maina Waziri.
Matsayar dattawan na PDP na nuna duk wani taro na takaita ‘yan takara irin wanda aka bukaci Janar Ibrahim Babangida ya jagoranta, da barin wasu a gefe, alhali suna da niyyar gwada farin jinin su, ba daidai ba ne.
Alhaji Sule Lamido ya ce rudanin ya shafi yadda shugaban kungiyar dattawan arewa Farfesa Ango Abdullahi ya fitar da sanarwa bayan wani taro da ya nuna an zabi mutum biyu a ‘yan takarar don wakiltar arewa da su ka hada da gwamna Bala Muhammad na Bauchi da tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki.
Kazalika Sule Lamido ya ba da tabbacin duk wanda Allah ya ba wa nasara a zaben fidda gwanin, za su mara masa baya.
In za a tuna Dr. Sadiq Umar Gombe na kungiyar dattawan ya ce su ma gayyato su aka yi su canko gwani a tsakanin ‘yan takara hudu, kazalika shi ma Janar Babangida ‘yan takarar ne su ka nemi ya zaba masu wanda ya fi cancanta.
Za a gudanar da taron fidda gwani na PDP ranar 28 da 29 ga Mayun nan.
Saurari rahoto cikin sauti daga Nasiru Adamu El-hikaya: