Shirin na wannan makon ya dora a inda ya tsaya a makon da ya gabata game da batun tsaro.
Ranar Larabar nan aka kaddamar da fara kamfen din ‘yan takarar shugaban kasa na babban zaben Najeriya da za a gudanar a watan Febrairun 2023.
Dage fara kamfen din jam'iyyar APC mai mulki daga Larabar nan zuwa wani lokaci nan gaba, ya haifar da yada raderadin cewa dan takarar jam’iyyar, Bola Tinubu, ne ba shi da lafiya.
Matsalar hare-hare da sace mutane don neman kudin fansa ta zama ruwan dare a sassan Najeriya inda ta hada har da Abuja, babban birnin kasar.
‘Yan Bokon arewacin Najeriya da su ka hada da malaman jami’a, ‘yan siyasa da jagororin addinai sun kaddamar da wata kungiyar da su ka yi wa taken “Arewa New Agenda” wato Sabuwar Alkiblar Arewa.
Shirin na wannan makon ya sake waiwayar kalubalen tsaro, musamman hanyar da za a magance matsalar satar mutane da ta zama ruwan dare da kuma sauran miyagun laifuka da ke yin barazana ga rayuka da dukiyoyin al’ummar jihohin arewa.
Alamu na nuna babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta yi matsayar hakura da rarrashin gwamnan Ribas Nyesom Wike da ke cewa lalle sai shugaban jam’iyyar Iyorchia Ayu ya sauka daga mulki don kujerar ta koma kudancin kasar.
Shirin Arewa a yau na wannan makon ya ci gaba da tattanawa akan binciken ‘yan takara don ganin ayyukan da suka yi na taimaka wa al’umma.
Shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP a Najeriya wanda ya yi murabus ya ce ya ajiye mukamin sa ne don samun sulhu a jam’iyyar, bisa korafin yawan mukamai a yankin arewacin kasar.
Masanin kimiyyar siyasar duniya na jami’ar Bayero ta Kano Dr. Sa’idu Ahmed Dukawa ya ce kasashen Afurka da dama za su yi juyayin mutuwar sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu don rawar da ta taka wajen karbar ‘yancin su.
Shirin wannan makon ya tabo batun illar yada jita-jita ko farfagandar karya ta hanyar daukar hirar wasu kamar ta zancen wayar tarho don isar da wasu sakonni da za a yi tsammani na sirri ne alhali duk shiri ne na muzanta wasu abokan hamayya.
Masana kimiyyar siyasa na bayyana cewa kalubalen tattalin arziki da matsalolin da ta gada daga gwamnatin Boris Johnson, su ne mafi girma dake gaban sabuwar Firai Ministar Burtaniya Liz Truss.
Matasa mazauna karamar hukumar Karu sun bayyana yadda dokar ta shafi rayuwarsu ta yau da kullum musamman masu kananan sana'o'in da su ke yi don samun kudin shiga.
Shugaban kungiyar JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bukaci gwamnatin Najeriya ta fitar da matsaya kan wadanda a ke tuhuma da hannu a kisan gilla ga babban malamin nan na Islama a Yobe Sheikh Gwani Aisami.
Kwararre kan aiyukan ganowa da hako man fetur Dakta Mubarak Ibrahim Mahmud, ya ce idan Najeriya za ta iya tace man da ta ke bukata a cikin gida, da arziki ya wadaci kasar.
Kasuwar canjin kudi ta Abuja da a ka fi sani da ZONE 4 ta yanke matsayar rage farashin dala daga sama da Naira 700 a makon jiya zuwa Naira 630.
Ana ci gaba da samun baraka a manyan jam'iyyun siyasa a Najeriya. Ta baya bayan nan da ta tsuduma cikin babbar rigima ita ce PDP wadda takaddamar Atiku da Wike ke girgiza ta.
Domin Kari