Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar Da Yakin Neman Zaben 2023 A Najeriya


Tinubu, hagu, Atiku dama (Hoto: Facebook: Kashim Shettima/Atiku Abubakar
Tinubu, hagu, Atiku dama (Hoto: Facebook: Kashim Shettima/Atiku Abubakar

Ranar Larabar nan aka kaddamar da fara kamfen din ‘yan takarar shugaban kasa na babban zaben Najeriya da za a gudanar a watan Febrairun 2023.

ABUJA, NIGERIA - Bisa jadawalin lamuran zaben, hukumar zabe ta tsaida ranar 28 ga watan nan ta zama ranar fara kamfen din ‘yan takarar shugaban kasa inda 12 ga watan gobe za ta zama ranar fara na gwamnoni.

Tuni wasu daga ‘yan takarar su ka shirya fara kamfen din tun daga sanyin safiyar Larabar nan don cin gajiyar kaucewa fafa gora ranar tafiya.

Dama can manyan ‘yan takarar jam’iyyu sun yi gangami a garuruwa daban-daban don ganawa da magoya bayan su don zama cikin shirin kaddamar da kamfen din.

Wani taron PDP da ta yi a baya (Instagram/PDP) an yi amfani da wannan hoto don nuna misali
Wani taron PDP da ta yi a baya (Instagram/PDP) an yi amfani da wannan hoto don nuna misali

Jami’ar labaru a hukumar zaben Zainab Aminu ta ce hukumar za ta zuba ido don kula da dokokin kamfen da a ka rattaba don gudanar da shi bisa ka’ida.

APC mai gwamnatin taraiya dai ta dage fara kamfen din har wani lokacin da ta ce za ta sanar duk da ba ta ce don dan takarar ta Bola Tinubu na ketare ba ne da hakan ya kawo raderadin ya je duba likita ne.

Salon Tinubu tun zaben fidda gwani shi ne bin hannun gwamnoni da ke da karfi a jihohin su. Ibrahim Masari tsohon mataimakin takarar Tinubun da su ke tare dare da rana, ya ce da gwamnoni za su gudanar da tafiyar daga farko har karshe.

Mahalarta taron kia kamfe gida-gida na jam'iyyar APC.
Mahalarta taron kia kamfe gida-gida na jam'iyyar APC.

Mataimakin shugaban babbar jam’iyyar PDP na arewa Umar Iliya Damagum ya ce sun shirya tsaf don kamfen mai tsabta kuma ya na da kwarin guiwar su na da goyon bayan jama’a.

Sauran ‘yan takarar jam’iyyun adawa irin Rabi’u Musa Kwankwaso a NNPP da Peter Obi a Leba na nuna za su iya tasiri kan manyan jam’iyyu biyu APC da PDP don samar da sabuwar babbar jam’iyya.

Matashiya da ke shugabantar mata a arewa maso yamma a jam’iyyar SDP Zainab Tijjani Baba ta ce a wannan karo ba sa shakkar jam’iyya mai gwamnati.

Shugaba Buhari da zai kammala wa’adi a mayun badi, ya yi alwashin damka ragama ga wanda jama’a su ka kadawa kuri’a.

Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-hikaya:

Yau Za A Kaddamar Da Yakin Neman Zaben 2023 A Najeriya.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG