ABUJA, NIGERIA - Taron na da zummar fidda jerin bukatun yankin arewa don mikawa duk ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.
Masana sun gabatar da jawabai kan tattalin arzikin yankin arewa da ya kunshi noma, kiwo, ma’adinai da yawan jama’a wadanda matukar a ka yi amfani da su yadda ya dace yankin zai farfado daga koma baya.
Shugaban sabuwar kungiyar Sanata Ahmed Muhammad Mo Allah-yidi ya ce su na son fadada muradun arewa ne fiye da yadda kungiyoyin yankin irin kungiyar tuntuba ta arewa da zauren dattawa su ke yi a halin yanzu.
Mo’ Allah-yidi ya ce za su rubuta jerin bukatun arewa su mika su ga duk manyan ‘yan takara da kuma zuba ido kan yadda za a yi da bukatun bayan lashe zabe.
Da ya ke magana Bishop Jonathan Ma’aji ya ce lallai arewa na da jan aikin dawo da yankin zamanin da ba a nuna bambanci a jamhuriya ta farko da a ka kifar a 1966.
Shi ma shugaban sulhu tsakanin addinai a Jihar Kaduna Barista Tahir Umar Tahir ya nuna kwarin gwiwar tafiyar za ta yi tasirin da a ke bukata ta farfado da yankin arewa daga rarrabuwar kawuna da rashin tsaro.
Duk gwamnonin da aka gayyata na arewa ba su halarci taron ba amma hakan bai rage armashinsa ba tun da daraktan gidan tarihin arewa wato “Arewa House” Shu’aibu Shehu Aliyu ya halarta da tawagarsa.
Saurari rahoton daga Nasiru Adamu El-hikaya: