Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mun Yanke Matsayar Dawo Da Farashin Dala Naira 630 Daga Sama Da 700-Kasuwar Canji Kudin Abuja


Abuja-Forex Bureau on Dollar rate.
Abuja-Forex Bureau on Dollar rate.

Kasuwar canjin kudi ta Abuja da a ka fi sani da ZONE 4 ta yanke matsayar rage farashin dala daga sama da Naira 700 a makon jiya zuwa Naira 630.

Matakin ya biyo bayan wani taro da shugabannin ‘yan kasuwar su ka yi da shugaban hukumar yaki da cin hanci EFCC Abdulrasheed Bawa.

‘Yan kasuwar sun yi gangami da amfani da amsa kuwwa wajen sanar da dukkan ‘yan kasuwar matakin da su ka ce ba don wani matsin lamba ba ne daga wata hukuma ko kuma kai tsaye a alakanta da samame da jami’an EFCC su ka kai kasuwar a watan jiya.

Mukaddashin shugaban ‘yan kasuwar Alhaji Shehu Liman ya ce duba yanda dalar kan yi sanadiyyar tashin farashin kayan masarufi ya jawo su ka daidaita don ba da ta su gudunmawar da za ta kawo sauki.

Abuja-Forex Market
Abuja-Forex Market

Tuni wasu daga fitattun ‘yan kasuwar da su ka hada da Alhaji Murtala Bashir su ka mika wuya ga matakin.

Shin wannan matakin zai iya shafar sauran manyan kasuwannin canji na Kano, Lagos, Fatakwal, Enugu da sauran su?

Alhaji Shehu Liman ya ce Abuja ce cibiya kuma nan take matakin da a ka dauka a birnin kan karade sauran sassa na kasa.

Liman ya ce za su rika bitar farashin dalar a duk mako don kara daukar matakan sauko da ita daga tashin gauron zabi har sai ta daidaita sahu da farashin gwamnati.

Za a zuba ido a ga tasirin matakin da ba shakka zai samu turjiya daga ‘yan jari hujja da kan amfana da tsadar wajen cin kazamar riba

Saurari rahoton Nasiru Adamu El Hikaya daga Abuja:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG