ABUJA, NIGERIA - Dr. Dukawa ya kara da cewa yawancin mutane sun tashi da jin sunan sarauniyar wacce ta zo da kan ta ziyarar aiki kasashen kuma ta kulla hulda mai karfi da manyan jagororin kasashen wadanda akasarin su, sun dade da barin duniya “duk mai shekara 40 zuwa 50 har 70 ya tashi ya na jin sunan sarauniya Elizabeth, don haka yau an wayi gari mai irin wannan matsayi ta kau daga duniya”.
Dukawa na ganin samun cike gurbin da marigayiyar ta bari na da wuya don yanda ta dade da samun gogewa a tsawon shekaru sai dai a na fata sabon sarki, magajinta Charles ya samu gogewa ko tarbiyantuwa daga mahaifiyar ta sa.
Marigayiya Elizabeth ta yi mu’amalar kirki da iyayen Najeriya irin marigayi Firai Minista Abubakar Tafawa Balewa da Firimiya Ahmadu Bello Sardauna har da ba su lambar girmamawa ta masarautar Ingila da aka ambatawa ko rubutawa gabanin sunan su wato SA ko kuma SIR a turance.
Saurari rahoto cikin sauti daga Nasiru Adamu El-Hikaya: