Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Na Yi Murabus Daga Shugabacin Kwamitin Amintattu Na PDP Don Kawo Sulhu – Walid Jibrin


Walid Jibrin (Channels TV)
Walid Jibrin (Channels TV)

Shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP a Najeriya wanda ya yi murabus ya ce ya ajiye mukamin sa ne don samun sulhu a jam’iyyar, bisa korafin yawan mukamai a yankin arewacin kasar.

Sanata Walid Jibrin wanda tuni mataimakinsa tsohon shugaban majalisar dattawa Adolphus Wabara ya karba a matsayin riko, ya nuna hakan ita ce sahihiyar hanyar kawo daidaito a jam’iyyar tsakanin arewa da kudu.

Jibrin na daga cikin wadanda su ke sahun farko a kafuwar PDP tun 1998 kafin fara mulkinta a 1999, don haka ya jaddada cewa zai iya sadaukar da kowane mukami don samun hadin kan jam’iyyar.

Fitinar jam'iyyar PDP ta taso ne tun lokacin da Atiku Abubakar ya samu nasarar zama dan takarar shugaban kasa kuma daga arewa, maimakon burin wasu ‘yan kudu irinsu gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike da ke son tikitin ya koma kudu.

Walid Jibrin ya ce murabus din nasa zai yi matukar rage cece-ku-ce kan mukaman jam'iyyar sun taru a arewa, ciki har da na shugaban jam’iyyar Iyorchia Ayu daga jihar Binuwai.

Shugaban amintattun PDP da ya yi murabus ya ce zai ci gaba da zama a jam’iyyar kuma zai samu babban mukami a yakin zaben dan takararsu Atiku Abubakar.

Matsayar shugaban jam’iyyar Ayu ita ce zai sauka bayan zaben 2023 in ya yi nasarar kai jam’iyyar ga gaci ta lashe zabe.

Mai magana da yawun Ayu Yusuf Dingyadi, ya ce ba zai yi murabus ba don hakan bahaguwar dabara ce ga fafutukar jam’iyyar ta neman dawo da madafun iko.

Yanzu dai za a jira a ga yadda Wike da magoya bayansa za su karbi murabus din na Jibrin, ko hakan zai sa su kawar da idon su kan Ayu.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG