Gwamnan jihar Binuwai Samuel Otom ya yi amfani da damar ganawa da gwamna Bala Muhammad na Bauchi wajen ba da hakuri ga kalaman da ya furta cewa sam ba zai zabi Bafulatani a matsayin shugaba ba, da cewa, gara ma ya mutu da ya goyi bayan Bafulatani.
Matasan sun ba da shawarin hanyoyin da za a bi wajen dawo da salama a Jihar ta hanyar saita kwakwalwar matasa zuwa dabi’u nagari.
Hukumar zaben wacce ta kammala zagaye na karshe na sabunta rejistar gabanin babban zaben 2023, ta baiyana filla-filla irin matakan da ta kan bi gabanin yin rejistar.
Shugabar kwamitin zabe ta Majalisar Wakilan Najeriya Aisha Jibir Dukku ta jaddada cewa, an tsara zaben 2023 ta hanyar da a ka toshe duk wata kafa ta magudi.
Dan takarar shugaban kasar Najeriya na jam’iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu, zai kaddamar da kamfen a ranar 15 ga watan Disamba a Jihar Filato bayan tsawon lokaci tun bude kamfen da hukumar zabe ta yi a ranar 28 ga watan Satumba.
Wata majiya ta ce jami’an sun tafi da akalla mutum 80 wadanda a lokacin hada wannan rahoto ake kokarin belin su.
Kan lamuran tsaro, Kwankwaso ya ce zai kara yawan jami’an sojoji zuwa miliyan daya haka nan ‘yan sanda ma za su zama miliyan daya.
Darajar Naira na kara kasa a canjin dala inda hakan ke karfafa fargabar kara tashin farashin muhimman kayan masarufi.
Magoya bayan ‘yan takarar shugabancin Najeriya na nuna yanda gwanayensu su ka yi zarra kan juna, yayin da kamfen din zaben 2023 ya fara kankama.
An samu mafi munin ambaliyar ruwa a ‘yan shekarun nan a Najeriya musamman in an kwatanta yawan mutanen da su ka yi asarar rayukansu. Mutuwar mutum 603 a fadin Najeriya ya ninka yawan wadanda su ka rasa rai a bara a sanadiyyar ambaliyar.
Ofishin dan takarar jam’iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso ya ce dan takarar na su ya ki zuwa zauren baje kolin manufofin ‘yan takara a gidan AREWA a Kaduna, don zargin taron na da manufar mara wa wani dan takara baya.
Mahmud Yakubu wanda ke magana a wata ziyara a Amurka a taron da asusun raya dimokradiyya da kuma asusun tallafawa tsarin zabe na duniya su ka shirya, ya ce labarun karya ya zama kalubale da ke kawo damuwa kan babban zaben Najeriya.
Ministan Cikin Gida na Najeriya Ra’uf Aregbesola ya ce Najeriya za ta rungumi hanyoyin kimiyya na tauraron dan-adam wajen kula da kan iyakokin kasar da tsawon su ya kai kilomita 5000.
Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana matukar takaici ga abin da ya zayyana a matsayin durkushewar al’adar karatun litttafai don samun ilimi mai inganci a tsakanin jama’ar da ke tasowa a wannan zamanin na yawaitar na’urorin sadarwa.
A wasu jihohin kamar Lagos an samu kimanin ‘yan takara 15 na gwamna daga jam’iyyu daban-daban ciki har da APC mai mulki da babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
Shirin ya tattauna da Ahmed Ibrahim Lau da kuma shugaban kungiyar fataken masara ta yankin arewa Modibbo Sadik Nafada.
Kazalika matasa sun zanta kan mahangar su ga yadda za a aiwatar da lamuran tsaro ta yadda zai yi tasiri ba tare da cutar da sauran jama’a da ke zaune lafiya ba.
Rundunar sojan Najeriya ta bayyana cewa ta tona rijiyar burtsatse mai aiki da hasken rana a kauyen Rinze da ke Akwanga a Jihar Nasarawa ne don kyautata huldar sojoji da fararen hula da zai taimaka ga samun bayanan sirri da su ka shafi tsaron kasa.
Duk da bude damar fara yakin neman zabe da hukumar zaben Najeriya ta INEC ta yi, ‘yan takarar manyan jam’iyyu da ke alwashin shiryawa tsaf don tinkarar zaben 2023 ba su kaddamar da kamfe ba.
Domin Kari