Dan takarar jam’iyyar NNPP a zaben shugabancin Najeriya na 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya kaddamar da muradunsa da yake so ya cin ma idan har Allah ya sa ya lashe babban zaben da ke tafe.
Daga cikin muradun akwai daukan matakin maida ilimi kyauta ga kowa da kowa.
Kan lamuran tsaro, Kwankwaso ya ce zai kara yawan jami’an sojoji zuwa miliyan daya haka nan ‘yan sanda ma za su zama miliyan daya.
“Hatta wadanda suka bijire da ke daji za mu yi kokarin jawo su don zama mutanen kirki da hakan zai ba da damar samar da tsaro mai dorewa.” In ji Kwankwaso.
A jawabin kaddamar da muradun nasa a Abuja, Kwankwaso ya ce zai bullo da tsarin da matasa za su samu ayyukan yi da kuma yaki da talauci.
Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-Hikaya: