ABUJA, NIGERIA - Zauren na gidan arewa da ke da gamayyar kungiyoyi na zama da dukkan ‘yan takarar shugabancin Najeriya, don faimtar irin alkawuran da za su yi ga arewa in an mara mu su baya.
A doguwar takarda da NNPP ta turawa zauren don bayyana dalilan rashin bayyana, ta ce ranar da a ka gayyaci Kwankwaso ta zo daidai da zuwan wani dan takara, inda bincike daga bisani ya nuna dan takarar PDP ne Atiku Abubakar.
Jigon kamfen din NNPP Buba Galadima, ya ce ba lalle sai Kwankwaso ya je zauren ne za a fahimci shi mai kishin arewa ne ko ya na da manufofi masu kyau don raya arewa ba.
Nan take daya daga masu shirya taron Hakeem Baba Ahmed ya nesanta Zauren da nuna bangare ya na mai cewa zargin ba shi da tushe.
Daraktan gidan arewa Dr. Shu’aibu Shehu Aliyu, ya ce kasancewar gidan na marigayi Sardaunan Sakkwato ne Sir Ahamdu Bello, duk mai manufar kwarai ga arewa na da hurumin ya zo ya baiyana manufofinsa.
A zaben nan na 2023 mai zuwa, an samu kungiyoyi na arewa masu nuna muradin gabatar da bukatun arewa ga ‘yan takara, don yanke hanzari ga korafin cewa rashin yin yarejeniya ke sa yankin ke tashi wayam kuma ba ikon yin komai.
Saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.