ABUJA, NIGERIA - Hukumar zaben Najeriya INEC ta fitar da jerin sunayen ‘yan takarar gwamna da na majalisun Jihohi, gabanin kaddamar da kamfen din su a hukumance a ranar 12 ga watan nan na Oktoba.
Hukumar ta ce ta sanya idanu kan dukkan zabukan kuma ta bar gurbin sunayen ‘yan takarar da ke shari’ar sahihin dan takara a kotu.
Jami’a a sashen labarun hukumar, Zainab Aminu ta ce, hukumar a shirye take ta cikata guraben da duk wadanda kotu ta yanke hukuncin su ne sahihan ‘yan takarar.
Bayan duba sunansa ya fito a jerin sunayen dan takarar gwamna na jam’iyyar hamaiya ta PRP a Katsina, Imran Jino, ya bukaci hukumar zaben ta dore da misalan da ta bayar musamman a irin zaben gwamnan Osun inda ‘yan adawa su ka karbi mulki daga APC.
Shi kuma dan takarar SDP a Adamawa Umar Ardo wanda shi ma ya ga sunan sa a jerin ‘yan takarar, ya yi hasashen a zaben 2023 magudi ma ba zai yi wu ba.
Za a gudanar da zaben gwamnonin da ‘yan majalisun jiha ranar 11 ga watan Maris din badi.
Babban zaben na Najeriya na 2023 zai fara da na shugaban kasa da ‘yan majalisar dokokin tarayya a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-hikaya: