Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tsara Zaben 2023 Ta Hanyar Da Ba Kofar Yin Magudi – Aishatu Dukku


AISHA DUKKU
AISHA DUKKU

Shugabar kwamitin zabe ta Majalisar Wakilan Najeriya Aisha Jibir Dukku ta jaddada cewa, an tsara zaben 2023 ta hanyar da a ka toshe duk wata kafa ta magudi.

Aishatu Dukku na magana ne a taron wayar da kai ga masu yada labaru na yanar gizo na mazabarta kan nagartattun hanyoyin yada labaru don gudanar da zaben bisa doka da oda.

Aishatu Dukku ta ce ko da wani ya yi karambanin rugawa da akwatin zabe don wargaza sakamako na aikin baban-giwa ne don na’ura kai tsaye na dauka da kidaya kuri’un da a ka kada.

Kazalika ta ce sabuwar na’urar na da tsarin gane mutum ta hanyar hoton sa ko da kuwa yatsun sa sun sude, saboda noma ko wani aikin kwadago.

‘Yar majalisar ta bukaci ‘yan Najeriya su fito su kada kuri’arsu ga duk wanda su ke so ba tare da shakkar rashin adalci ba.

Yayin da ta ke gargadin masu yayata labarun na yanar gizo da gujewa yada labarun karya ko na cin zarafin wani dan takara, Dukku ta ce doka ta tanada daurin wata 6 ko biyan tarar Naira dubu 100 ga duk wanda ya yi karantsaye ga yada labarun zabe.

Taron Wayar Da Kai Ga Masu Yada Labaru Na Yanar Gizo
Taron Wayar Da Kai Ga Masu Yada Labaru Na Yanar Gizo

Masanin kimiyyar siyasa na Jami’ar Abuja, Dakta Abubakar Umar Kari, ya duba irin labarun da ba a iya kauce mu su a kafafen labarun na yanar gizo da kuma ke da tasiri a zaben.

Kari ya ce labarun sun hada da bangaranci, kabilanci da bambancin addini.

A nan Dakta Kari ya shawarci masu zabe su duba abubuwan da ‘yan takarar su ka yi a baya don ganin wanda za su kadawa kuri’a.

Hukumar zabe ta bayyana cewa, kafafen yada labarun yanar gizo musamman masu yada jita-jita na kawo babbar barazana ga shirin zaben.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

XS
SM
MD
LG