ABUJA, NIGERIA - Duk da haka wasu masu sharhin siyasa na bayyana bin kamfen din da mutunta juna, musamman bayan ganin kicibis din da dan takarar jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya yi da dan takarar babbar jam’iyyar adawa PDP Atiku Abubakar a filin saukar jiragen sama na Abuja, su ka kuma gaisa cikin raha.
‘Yan takarar manyan jam’iyyun biyu dai a can baya sun taba zama a jam’iyya daya don a zaben shekara ta 2007. Atiku Abubakar ne ya tsaya takara a jam’iyyar ACN yayin da Tinubu ya ke jigon jam’iyyar kuma gwamnan Jihar Lagos.
Jagoran “a Kasa a tsare” na shugaba Buhari, Injiniya Kailani Muhammad, ya ce zabar Tinubu a 2023 shi ne mafi a’ala ga Najeriya.
Shi ma jigon NNPP Buba Galadima na maimaita cewa gwaninsa Rabi’u Kwankwaso ne zai iya lashe zaben ko da hakan zai kai ga zuwa zagaye na biyu.
A bangaren PDP, jigon kamfen din Sanata Abdul Ningi ,ya ce ba wanda ya kai Atiku Abubakar cancantar amsar ragamar Najeriya a wannan karon.
Sauran ‘yan takara irinsu Peter Obi na Leba na kokarin nuna tafiya da matasa da kore batun bangaranci.
Masana na ganin zaben na 2023 zai ba da mamaki don yadda manyan ‘yan takara su ka rabu a sassan Najeriya da kuma fitowa daga manyan kabilun kasar.
Saurari cikakken rahoton daga Nasiru Adamu El-hikaya: