Wani lauya a Abuja, Barista Mainasara Kogo Umar, ya bayyana cewa shekara ta 2022 mai bankwana na daga cikin shekarun da ‘yan Najeriya ba su samu wani canji mai ma’ana ba.
‘Yan takarar mukamai daban-daban a zaben 2023 na jan hankalin magoya baya wajen ambata alkawuran canji da za su kawo in an ba su dama.
Shirin ya duba abubuwan da su ka karkace da in an saita su, yankin arewa ka iya farfadowa daga matsalolin da ya shiga da ba a yi tsammanin su ba a tarihin baya.
A cigaba da yakin neman zaben sabon shugaban Najeriya a ranar 25 ga watan Febrairu mai zuwa, ‘yan takarar manyan jam’iyyu da magoya bayan su na bayanan abubuwan da a ke ganin za su haddasa mu su cikas.
Wani kwamitin bincike na mutum 7 da shugaba Buhari ya kafa a asirce don duba ayyukan tara kudaden shiga na yau da kullum na bankuna, ya gano zunzurutun kudi da su ka kai dala biliyan 171 da babban bankin Najeriya ya ajiye a wani asusun da baya amfanar gwamnati.
Hukumar kwastam ta Najeriya ta bayyana cewa yakin Ukraine ya kawo koma baya wajen kammala tara kudin shiga da gwamnati ke son hukumar ta tara da su ka kai Naira tiriliyan 3.1.
Hukumar kwastam ta ce a fili ta ke gudanar da gwanjan kaya kuma kowa zai iya shiga yanar gizo ya ga yanda a ke gudanar da cinikin.
Kungiyar ta Miyetti Allah, ita ce uwar kungiyar da ke kula da alma'muran mafi aksarin Fulanin Najeriya wadanda suke zaune a sassan kasar.
Madugun kamfen din samun tikitin dan takarar APC Bola Tinubu, Babachir David Lawan ya fito karara ya ce bai ga yadda Tinubu zai lashe zaben 2023 ba tun da bai dauki kirista mataimaki ba.
Zaben sabbin shugabannin uwar kungiyar Fulani makiyaya ta “MIYETTI ALLAH” ya bar baya da kura don daya daga ‘yan takara ya ce bai amince da sakamakon zaben ba.
Samame a kasuwar canjin ya haddasa sanya wasu ‘yan kasuwar buya inda har ta kai ga EFCC ta kama wasu daga cikin ‘yan kasuwar amma daga bisani ta sake su.
Dama jihar na fuskantar kalubalen tsaro daga musamman masu satar mutane da a ka fi fama da su a sassan karamar hukumar Isah da Sabon Birni.
Matasan sun ba da shawara kan hanyoyin da za a bi wajen dawo da salama a jihar ta hanyar saita kwakwalwar matasa zuwa dabi’u nagari.
Yayin da aka yi bankwana da ambaliyar ruwa a wasu sassan duniya, har yanzu akwai fargabar wannan matsalar da dangoginta a sassan Najeriya
Domin Kari