Shirin na wannan makon ya kunshi bayanai masu muhimmanci game da inganta rayuwar matan arewa ta hanyar karfafa shigar da su makaranta da kuma koyawa wadanda ba su samu damar hakan ba sana’o’in hannu don su zama masu dogaro da kai.
An fahimci cewa rashin shigar da mata masu yawa makaranta a arewa na daga cikin abubuwan da ke kawo wa mata koma baya da maida su rayuwar hannu baka hannu kwarya.
Saurari shirin cikin sauti: